Hadakar kungiyoyi ta samarin Arewa ta baiwa kabilar Ibo mazauna Arewa watanni uku su fice daga yankin

Hadakar kungiyoyi ta samarin Arewa ta baiwa kabilar Ibo mazauna Arewa watanni uku su fice daga yankin

- Hatsabibai a Arewa na son ballewar Najeriya

- Dama dai auren dole ne turawa sukayi wa kabilun Najeriya

- Suma mutan Ibo sun sha nuna son ballewar Najeriya

A sanarwar da suka fitar, wasu samarin Arewa masu kiran kansu hadakar kungiyoyin matasan Arewa, sun fitar da sakamakon taronsu da cewa, sun baiwa 'yan kabilar Ibo mazauna Arewar, wananni ukku kacal su hada nasu-ya-nasu su fice daga yankin.

Sun kuma yi kira ga mutan Arewa mazauna kudancin Najeriya da suma su taho gida daga 1 ga watan Okboban banar nan.

KU KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar

Hatsabiban ta bakin shugabansu Alhaji Abdul'aziz Suleiman, sun ce sun gaji da kurari daga wasu hatsabiban daga Kudu irin su Nnamdi Kanu ke yi na sai sun balle daga Najeriya, inda suma suka ce a rabun, don sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba.

Ga dukkan alamu dai, suma suna so su dan bada tsoro ne su kuma nuna Arewar bata dogara da arzikin da ake sha daga kudun ba, kuma suna ma ganin arewar zata iya tsayawa ita kadai.

"Muna kira da babbar murya, ga duk hukumomi na Najeriya, su ji mu da kyau, daga 1 ga Okboban banan nan, bamu cikin duk wani tsarin kasa mai suna Najeriya, da zai hada da 'yan kabilar Igbo a cikinsa" Sanarwar tace.

Yaro dai man-kaza, inji mai iya hangen nesa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel