Mijina cizo yake duk lokacin da muke fada, a raba mu - Wata mata ta fadawa kotu

Mijina cizo yake duk lokacin da muke fada, a raba mu - Wata mata ta fadawa kotu

- Wata mata mai suna Kudirat Sodiq ta fadawa kotu cewa maigidanta wahabi da cizo ya ke binta a duk lokacin da suka samu rikici.

- Matar wadda ta shigar da kara wata kotu da ke Igando a jahar Lagos ta shaidawa kotun cewa jikin ta cike yake da tabon cizon da maigidan na ta ke yi mata, saboda idan ya fara ba ya barin ta sai ya ga jini ya na fita daga jikin ta.

Kudirat ta shaida wa kotun cewa mai gidan nata na tsahon shekara 23 kullum a cikin maye yake daga shan barasa da zukar tabar wiwi.

A fadar ta “Akwai lokacin da ya zo shagon sana’a ta dauke da kwalbar giya inda ya fasa ya nemi kashe ni, sai na tare da hannuna, har na ji ciwo.

“Bayan haka kuma ya yi ta yunkurin siyar min gidana da na gina, bai samu nasara ba”

Mijina cizo yake duk lokacin da muke fada, a raba mu - Wata mata ta fadawa kotu

Mijina cizo yake duk lokacin da muke fada, a raba mu - Wata mata ta fadawa kotu

NAIJ.com ta samu labarin cewa ta ce kullum a cikin tsoro ta ke duba da yadda Wahabi ke yin barazanar zai kashe ta a ko dai yaushe, a don haka ne ta yi kira ga kotun da ta gaggauta raba auren domin ta ci gaba da rayuwar ta.

A nashi bangaren, Wahabi ya zargi matar shi da bin maza, inda ya bada misalin wani lokacin da yaje shagon sana’arta ya ga wani mutum ya na yanke farcen shi. Ya ce da mutumin ya gan shi sai ya bar gurin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel