Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

- Jami’ar Sojin kasa dake garin Biu zata fara aiki a watan Satumba

- Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

Jami’ar Sojin kasa dake garin Biu zata fara aiki a watan Satumbar bana, inji babban hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Buratai ya bayyana haka ne bayan ya karbi takardun filayen jami’ar da taswirar ginin jami’ar daga hannun gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Litinin 5 ga watan Yuni a garin Maiduguri.

KU KARANTA: Shiriya daga Allah: Sarauniyar kyau ta Musulunta

Buratai ya kara da cewa tuni sun mika kokon bararsu ga hukumar kula da jami’o’in kasar nan domin samun daman tabbatar da jami’ar, sa’annan Buratai yace kwararrun injiniyoyin Sojin kasa sun fara gudanar da ayyukan gine gine a Jami’ar.

Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

Buratai da Kashim

Babban hafsan ya jinjina ma gwamnatin jihar Borno sakamakon goyon bayan da suke baiwa hukumarsa, inda ya kara da cewa an samar da kudaden ginin jami’ar a kasafin kudin bana.

Daga karshe Buratai yace an tsara jami’ar ne domin samar da mafita da warware duk wasu matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso gabas, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta jiyo.

A nasa jawabin, Shettima ya tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa bakin gwargwado don ganin an samar da jami’ar, inda yace muddin an kammala jami’ar, tabbas zata zama abin koyi a nahiyar Afirka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya alakar Yansanda da jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel