Kasar Kamaru ta tsare wasu sojojin da ke yaki da Boko Haram

Kasar Kamaru ta tsare wasu sojojin da ke yaki da Boko Haram

- Kasar Kamaru tace ta kama wasu sojojin kasar wadanda ke yaki da kungiyar ‘yan ta’adda Boko Haram saboda boren da suka yi

- Sojojin sun yi bore ne kan kin biyan su wasu kudade na alawus da na hutu

- Gwamnatin kasar ta ce an kwashe sojojin daga yankin Zique zuwa birnin Yaounde, in da ake tsare da su

Hukumomin kasar Kamaru sun kama akalla sojoji 30 da ke yaki da kungiyar ‘yan ta’adda Boko Haram saboda boren da suka yi kan kin biyan su wasu kudade na alawus da na hutu.

Sojojin sun yi bore a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni da ta gabata a yankin arewacin kasar, in da suka tare hanyoyin zirga-zirgar motoci.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, ma’aikatar tsaron kasar ta ce, yanzu haka an kwashe sojojin daga yankin Zique zuwa birnin Yaounde, in da ake tsare da su.

Kasar Kamaru ta tsare wasu sojojin da ke yaki da Boko Haram

Sojojin da ke yaki da Boko Haram

Rahotanni sun ce, harkokin yau da kullum sun koma yadda aka saba bayan boren sojojin.

KU KARANTA: Harin Boko Haram ya kashe mutane 21 a kusa da Chibok

A wata bangare kuma daruruwan ‘yan gudun hijira na cikin gida a arewacin kasar Kamaru, suna kauracewa sansanan dake kusa da kan iyaka da Najeriya saboda rashin isashen tsaro a sansanin, bisa ga cewarsu, yanzu rayuwarsu na cikin hadari, biyo bayan hare-haren kunar bakin wake da aka kai, yayin da gwamnati ke kira da a kwantar da hankali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kudancin kaduna kashi na biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel