Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar

Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar

- Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, ana sa ran cewa shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar mai zuwa

- A yau Talata ne uwargidan shugaban kasa ta dawo daga birnin Landan bayan ziyara da ta kai ma mijin nata

- Ta nuna godiya ga ‘yan Najeriya bisa ga addu’oin su ga maigidanta

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, ana sa ran cewa shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar mai zuwa.

NAIJ.com ta tuna cewa a ranar 7 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari ya tafi birnin London don duba lafiyarsa bayan ya mika ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

KU KARANTA KUMA: Reno Omokri ya kai hari ga Lai Mohammed

Har ila yau a safiyar yau Talata ne uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya bayan ta kai wa maigidan nata ziyara a can inda yake jinya wato birnin Landan.

Ta kuma sanar da cewa shugaba Buhari na samun sauki sosai kuma zai dawo nan bada jimawa ba domin ya daura daga inda ya tsaya.

Daga karshe kuma ta yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa tarin addu’oi da kuma fatan alkhairi da suke yi ga maigidan nata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo kan ra'ayin jama'a dangane da dawowar shugaba Buhari a nan kusa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel