Za’a sa zaren dambe tsakanin Dogara da Floyd Mayweather

Za’a sa zaren dambe tsakanin Dogara da Floyd Mayweather

- Yakubu Dogara zai dambace da ɗan Damben Amurka Floyd Mayweather

- Floyd Mayweather ya kawo ziyarar kwanaki uku Najeriya

Za’ayi wani damben abota tsakanin Kaakakin majalisar wakilai Honorabul Yakubu Dogara da fitaccen dan damben nan na Amurka Floyd Mayweather.

Shago Dogara da Mayweather zasu fafata ne a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni a kasaitaccen masaukin nan dake babban birnin tarayya, Abuja, Transcorp Hilton.

KU KARANTA: Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

Manufar damben shine, barje gumi domin a tattara kudade domin aikace aikacen tallafi da wata gidauniya take yi.

Za’a sa zaren dambe tsakanin Dogara da Floyd Mayweather

Dogara

Majiyoyi da dama sun tabbatar ma NAIJ.com cewar Yakubu Dogara ya amince ya fafata da tsohon dan damben.

Shugaban kamfanin Tetrazzini, Donatus Okonkwo ne ya bayyana haka a wajen wani taron manema labarai a garin Abuja a ranar Litinin 5 ga watan Yuni, inda yace suna fatan karawar za ta yi armashi.

Za’a sa zaren dambe tsakanin Dogara da Floyd Mayweather

Floyd Mayweather

Donatus ne gwannin shiryawa da daukan nauyin kawo Floyd Mayweather Najeriya a ziyarar kwanaki uku da zai kawo don bikin wasan dambe a Najeriya.

Ana sa ran Mayweather zai kai ziyara jihohin Legas, Anambra, Akwa Ibom da Abuja inda zai gana da bangaren zartarwa da majalisar dokoki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya batun auren bare?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel