Budeden wasika zuwa ga ministan matasa da wasanni Bar. Solomon Dalung

Budeden wasika zuwa ga ministan matasa da wasanni Bar. Solomon Dalung

- An tir da martanin da ministan matasa da wasanni ya yi wa Sheikh Isa Ali Pantami cewa bai masa adalci ba kan kiran ya musulunta

- Marubucin ya ce abin da Sheikh Pantami ya yi abunda ya wajaba akansa ne na kira zuwa ga kalmar Allah

- Acewar marubucin zuwan shi wajen taron addinin musulunci ba zai kari ko ragi musulmai da komai ba

Ka ce gayyatar da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi maka zuwa shiga addinin musulunci bai yi maka adalci ba.

Sheikh Pantami, ya yi abunda ya wajaba akansa ne na kira zuwa ga kalmar Allah, kuma kai ka kawo kanka wajen da yake wannan kira, ba wanda ya gayyace ka, baice maka dole sai kayi musulunci ba, nasiha ya maka cikin ilimin addinin musulunci domin sheikh Pantami yana neman ka zuwa ga rahamar Ubangiji ne.

Toh meye abun laifi ko rashin adalci a nan?

Budeden wasika zuwa ga ministan matasa da wasanni Bar. Solomon Dalung

Ministan matasa da wasanni Bar. Solomon Dalung

Idan baka son ayi maka kira zuwa musulunci sai ka dai na zuwa wajen karantarwar musulmai domin ko kaje ko baka jeba addinin musulunci yana kira ga wadanda ba suyi imani ba su yi imani.

Zuwan ka ko rashin zuwan ka wajen taron addinin musulunci bazai kari ko ragi musulmai da komai ba, domin haka katsa a gefen ka na kirista kar ka kuskura kana shiga hurmin addinin mu, domin ba kada ilimi akan musulunci kana magana ne irin ta son rai da neman bata mana addini kuma anyi walkiya mun gane abun da yake kai ka masallatai dan haka ba zamu bari saboda alakar mu da kai ta siyasa ko fafutuka ba yasa mu kaucewa karantarwar addinin mu ba.

KU KARANTA: Ban ji daɗin yadda Pantami yayi min tayin shiga Musulunci ba – Inji Solomon Dalung

Wannan shine sako na gare ka Solomon Dalung, a matsayi na wanda muka yi shekaru muna gwagwarmaya da kai a harkar siyasa da fafutukar duniya. Inji Affan Buba Abuya

A makon data gabata ne dai NAIJ.com ta ruwaito muku ministan ya kai ziyara a Masallacin Annur dake Abuja inda Sheikh Pantami Pantami ke gabatar da Tafsir cikin watan azumi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gidan talabijin na NAIJ.com ta tambayi mutane ko ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakinsa mulki kamar yadda wasu 'yan Najeriya ke cewa, ku ji ra'ayoyin su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel