Wajibi ne ‘yan Najeriya su daina kashe sauro – Farfesan ilimin kwari, Adeolu Ande

Wajibi ne ‘yan Najeriya su daina kashe sauro – Farfesan ilimin kwari, Adeolu Ande

-Wani farfesan ilimin kwari na jami’ar Iloro, Adeolu Ande yayi gargadi kan kisan sauro.

A wata jawabin da ya gabatar a taron da jami’ar ta shirya ranan Litinin, Ande yace akwai ilimi da yawa da ya kamata da dan Adam ya dauka daga kwari.

Yace: “ Rayuwan dan Adam ba zai yiwu ba tare da kwari ba kuma wannan ya taimakawa rayuwan mutum kuma ya cutar da shi.

“Cututtuka irinsu rashin lafiya, asaran amfanin gona, lalacewan abinci, da sauran su wanda bai wuce kasha 5 cikin 100 ba amma mutane suna wuce gona da iri wajen kashe su.”

Wajibi ne ‘yan Najeriya su daina kashe saurio – Farfesan ilimin kwari, Adeolu Ande

Wajibi ne ‘yan Najeriya su daina kashe saurio – Farfesan ilimin kwari, Adeolu Ande

Ande yace amfanin da suke da shi ya kunshi taimakawa girman fire, sake amfani da datti,wanda ake amfani da shi wajen kera magunguna, sinadarai da sauran su.

Yace: “ Hakikanin gaskiya shine su kansu kwarin basu da lafiya amma suna cutar da mutane da abubuwan gona ne ba da sani ba.

KU KARANTA: Ba ruwanmu da jam' iyyar APDA - PDP

“Misali shine sauro wanda ke zuwa zukan jini domin ciyar da ‘ya’yan da zata haifa.

“Manyan matan sauro suna girmama ‘yayansu sosai wanda ke sanyawa suna daukan kasadan rayuwa wajen neman abinci.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel