Reno Omokri ya kai hari ga Lai Mohammed

Reno Omokri ya kai hari ga Lai Mohammed

- Lai Mohammed ya ce babu wanda zai iya kalubalantar ayyukan gwamnatin tarayya zuwa yanzu

- Omokri ya ce zai kalubalancin ministan sannan ya tabbatar masa da cewa shi (Lai) makaryaci ne

- Lai Mohammed ya ce babu wanda zai iya kalubalantar ayyukan gwamnatin tarayya zuwa yanzu

Reno Omkri ya soki Lai Mohammed, sakamkon ikirari da ministan ya yi na cewa babu wanda zai iya karyata hujoji da ya gabatar ga ‘yan Najeriya zuwa yanzu.

Tsohon mataimakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a shafukan zumunta ya saki sabon bidiyo wanda a ciki ne ya lissafa karairayi guda biyar da ministan bayanai da al’adu ya fada ma ‘yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Fani-Kayode ya soki Osinbajo kan rashin halartan taron ECOWAS

Omokri wanda ya bayyana cewa ministan ya shahara gurin zuba karya, ya ce a shirye yake yak are kansa a kotu idan Lai Mohammed ya kai masa sammaci kan halayensa da ya fadi.

Kalli bidiyo wanda a ciki ne Omokri ya lissafa karairayi biyar da Lai Mohammed ya yi.

Kwanan nan Omokri ya soki shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da kalamai masu zafi.

Ya je shafin san a Facebook, ya kwatanta tsakanin Donald Trump da shugaba Buhari da kuma rayuwarsu kafin shugabanci.

Kalli bidiyon NAIJ.com wanda a ciki yan Najeriya suka maida martani game da yiwuwar dawowar shugaba Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel