Ambaliyar ruwa a jihar Niger: Wasu sun mutu inda dubunai suka rasa matsuguni

Ambaliyar ruwa a jihar Niger: Wasu sun mutu inda dubunai suka rasa matsuguni

- Ambaliyar ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwan mutane shidda a wasu garuruwa dake karkashin kananan hukumomi uku a jihar Niger

- Kananan hukumomin da ambaliyar ya faru sun hada da Mashegu Borgu da kuma Agaie

- Gwamnatin jihar Niger ta ce ta fara shirin kai agaji ga wadanda lamarin ya shafa

Rahotanni sun kawo cewa ambaliyar ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwan mutane shidda a wasu garuruwa dake karkashin kananan hukumomi uku a jihar Niger.

Zuwa yanzu daruruwan mutane sun rasa gidajensu tare da dukiyoyinsu sakamakon afkuwar mummunan al’amarin.

Ambaliyar ruwan ya faru ne a kananan hukumomin da suka hada da Mashegu Borgu da kuma Agaie

KU KARANTA KUMA: Fani-Kayode ya soki Osinbajo kan rashin halartan taron ECOWAS

Shugaban karamar hukumar Mashegu Alhaji Sa’idu Shu’aibu Kaboji, ya koka kan cewa akwai kimanin mutane dubu shida wadanda basu da gidaje da abincin da zasu ci duk da har yanzu ba a kammala kididdiga ba.

Yayinda a karamar hukumar Bargu kuwa, ambaliyar ta rufta gidaje sama da 200, haka kuma anyi asarar dukiya na dabbobi masu yawan gaske.

Gwamnatin jihar Niger ta ce ta fara shirin kai agaji ga wadanda lamarin ya shafa, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Niger Alhaji Ibrahim Inga, ya ce yanzu haka suna kokarin samarwa da mutanen abinci da guraren kwana na wucin gadi.

Tuni rahoton masu hasasshen yanayi suka nuna cewa jihar Niger na daya daga cikin jihohin da za a samu ambaliyar ruwa.

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel