‘Yan gudun hijira na kauracewa sansanonin da ke kusa da Najeriya

‘Yan gudun hijira na kauracewa sansanonin da ke kusa da Najeriya

- Wasu ‘yan gudun hijira da ke kan iyaka da Najeriya na kauracewa sansanonin su domin yawan hare-haren ta’addanci a sansanin

- ‘Yan gudun hijiran na cewar yanzu rayuwarsu na cikin hadari domin babu tabbacin tsaro a sansanin

- Kasar Kamaru ta ce kimanin mutane 150 suka kauracewa sansanin da aka tsugunar da su

Daruruwan ‘yan gudun hijira na cikin gida a arewacin kasar Kamaru, suna kauracewa sansanan dake kusa da kan iyaka da Najeriya, bisa ga cewarsu, yanzu rayuwarsu na cikin hadari, biyo bayan hare haren kunar bakin wake da aka kai, yayin da gwamnati ke kira da a kwantar da hankali.

Fiye da mutane 10 suka mutu da suka hada da ‘yan kunar bakin waken, 30 kuma suka ji raunuka.

Samari Bakassia wani magidanci dan shekaru 40 wanda matarsa ta rasu a harin, ya ce ya kauracewa sansanin ne da jaririyarsa ‘yar wata 2 sabili babu tabbacin tsaro a sansanin.

Ya ce suna cikin dimuwa, yanzu suna dogara ga Allah ya cecesu daga hannun ‘yan ta’addan.

‘Yan gudun hijira na kauracewa sansanonin da ke kusa da Najeriya

Wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da Najeriya

KU KARANTA: Aisha Buhari ta dawo daga kasar Ingila, tayi magana kan jikin Buhari

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamnatin kasar Kamaru ta ce kimanin mutane 150 suka kauracewa sansanin da aka tsugunar da ‘yan kasar Kamaru 500, dake gudun mayakan Boko Haram.

Majalisar Dunkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin ‘yan kasar Kamaru dubu maitan suka rasa matsugunansu sakamakon tashin hankalin Boko Haram, kashi 40 cikin 100 kuma kanananan yara ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel