Fani-Kayode ya soki Osinbajo kan rashin halartan taron ECOWAS

Fani-Kayode ya soki Osinbajo kan rashin halartan taron ECOWAS

- Femi Fani-Kayode ya soki mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, kan rashin halartan taron shugabannin ECOWAS wanda aka gudanar a ranar Asabar

- An gudanar da taron ne a Monrovia, babban birnin kasar Liberia, wanda ya samu halartan Priministan HKI, Benjamin Netanyahu

- Ya bayyana rashin halartan shugaban a matsayin abun bakin ciki da kunya ga Najeriya

Tsohon ministan dake kula da tashi da saukan jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode ya soki mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, kan rashin halartan taron shugabannin ECOWAS wanda aka gudanar a ranar Asabar.

An gudanar da taron ne a Monrovia, babban birnin kasar Liberia, wanda ya samu halartan Priministan HKI, Benjamin Netanyahu.

KU KARANTA KUMA: Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

Fani-Kayode ya soki Osinbajo kan rashin halartan taron ECOWAS

Fani-Kayode ya soki gwamnatin Buhari kan rashin halartan taron ECOWAS

Netanyahu ya kasance shugaban kasar da ba na Afrika ba na farko da aka gayyata domin ya yi jawabi ga shugabannin ECOWAS.

Zuwa yanzu babu wani jawabi daga fadar shugaban kasar Najeriya, kan dalilin da ya sa ba’a wakilci kasar a gurin taron ba.

Fani-Kayode ya rubuta a shafin san a twitter: “Ba daidai bane a ce @ProfOsinbajo bai halarci taron shugabannin ECOWAS ba tare da @netanyahu a yau. Rashin zuwan Najeriya abun bakin ciki ne da kunya.”

A halin da ake ciki NAIJ.com ta samu labarin cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya halarci taron. Amma babu wani bayani dake nuni ga cewa ya je taron ne don wakilci Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon hira da Fani-Kayode ya taba yi da shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel