Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

- Garba Shehu, ya yi watsi da wani rubutu da wani marubuci ya yi, wanda ya nuna cewa an yi wata cukurkudaddar yarjejeniya dangane da shugabancin kasar

- Ya yi watsi da rubutun da Max Siollun ya yi a matsayin rade-radi kawai

- Ya ce babu alaka tsakanin rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta marigayi Umaru Yar’Adua

Babban mataimakin shugaban kasa a kafofin watsa labarai Garba Shehu, ya yi watsi da wani rubutu da wani marubuci ya yi, wanda ya nuna cewa an yi wata cukurkudaddar yarjejeniya dangane da shugabancin kasar Najeriya, wadda za ta iya raba kan kasar.

Malam Garba Shehu, ya yi Allah wadai da rubutun da Max Siollun ya yi a matsayin rade-radi kawai, wadda aka buga a wata mujalla mai suna Foreign Policy, da ke Amurka.

Ya kara da cewa marubucin ya kirkiri karya ne kawai shaci-fadi dangane da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma halin da kasar ke ciki a hannun mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya bar wa mulki kafin ya tafi.

Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta ce babu wani rudanin shugabanci a rashin lafiyar Buhari

“In banda son ya saka mutane cikin rudani, me zai sa shi danganta rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta marigayi ‘Yar’Adua?” Shehu ya ce yanayin ma kwata-kwata ba iri daya ba ne.

Ya kara da cewa shi fa Shugaba Buhari kafin ya koma Ingila ya bayar da mulki a matsayin riko ga mataimakinsa kamar yadda doka ta tanadar.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta dawo daga kasar Ingila, tayi magana kan jikin Buhari

Ya yi nuni da cewa shi kuwa ‘Yar’Adua ai lokacin da rashin lafiya ta ci karfin sa, ai ba shi ma da sukunin iya mika mulki.

Don haka ya ce tunda shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki a hannun mataimakin sa, to maganar cewa ya bar gibin shugabanci wanda hakan zai iya harfar da rudanin shugabanci, bai ma taso ba.

Don haka sai ya ce jama’a su daina kitsa rudani da karairayi, tunda mukaddashin Shugaban Kasa ya na gudanar da aikin sa babu wani cikas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo kan ra'ayin jama'a dangane da dawowar shugaba Buhari a nan kusa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel