Jami’iyyar PDP ta nisanta kanta da sabon jam’iyyar APDA

Jami’iyyar PDP ta nisanta kanta da sabon jam’iyyar APDA

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta misanta kanta daga sabuwar jam’iyyar da aka kaddamar jiya mai suna Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA).

APDA, wata sabuwar jam’iyya ce da aka kaddamar a ranan Litinin wanda babban jigon PDP, Raymond Dokpesi, ya halarci taron.

A wata jawabin da kakakin jam’iyyar , Dayo Adeyeye, ya saki yace ba ruwan jam’iyya PDP da sabuwar jam’iyyar.

Jami’iyyar PDP ta nisanta kanta da sabon jam’iyyar APDA

Jami’iyyar PDP ta nisanta kanta da sabon jam’iyyar APDA

“Sa’o’in da suka wuce, mun samu kiraye-kirayen waya daga mambobin jam’iyyarmu, abokan arziki akan cewa shin munada alaka da sabuwar jam’iyyar Advance Peoples Democratic Alliance (APDA) da aka kaddamar yau a Abuja.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta dawo daga kasar Ingila

“Muna fadi ba babban murya, babu ruwan mu da sabuwar jam’iyyar da aka kaddamar. APDA ba wata reshen PDP bane kuma ba sabuwar jam’iyyarta bane kamar da yadda ake radawa.”

“Muna wannan jawabi ne domin bayyanawa mutane da kuma kawar da rade-radin banza da zai kawo rabuwan kai tsakanin mambobin jam’iyyarmu,”.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel