Azumin Ramadana: Hukuma ta gargadi malamai kan zafafa wa'azi

Azumin Ramadana: Hukuma ta gargadi malamai kan zafafa wa'azi

- A lokutan Ramadana dai ana wa'azi, da kokarin komawa ga Allah

- Wasu malaman addini na amfani da wannan dama su zafafa wa samari ra'ayi

- Haka Boko Haram ta shafe shekaru tana wa'azi a kan idon hukuma da mutan gari

A Jihar Kano ta arewacin Najeriya, hukumar 'yansanda ta fidda sanarwa ga masallatai da dakunan wa'azi ta bakin kakakinta, Magaji Musa Majiya, inda tace ya kamata a kuka da kai a kiyayi wa'azi mai tunzura jama'a ga bore ga gwamnati ko hakon jama'a.

Sanarwar na zuwa ne lokacin da malamai suka dukufa da tafsiri, da niyyar jawo mutane kusa da addini, da gudan abun-qi. Sai dai a wasu lokutan malaman kan zaqe har su yi wa'azi da zai shuka kiyayya a cikin al'umma, a bisa banbancin al'ada, addini, kabila, ko ma darika.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta roki kasar Indonesia da ta sauya hukuncin kisa da aka yanke wa ‘Yan Najeriya 300

Azumin Ramadana: Hukuma ta gargadi malamai kan zafafa wa'azi

Azumin Ramadana: Hukuma ta gargadi malamai kan zafafa wa'azi

Kakakin hukumar ya kara da cewa:"Hukumarmu ta baza jami'ai na boye da na fili zuwa dakunan wa'azi, domin jiyo wa hukuma waye ke son tada zaune tsaye, waye kuma ke son yada fitina a al'umma, don haka a kula."

Ya kuma yi kira ga jama'a da hukumomin masallatai su saka ido kan shige da fice da zirga-zirgar jama'a don cafko bata-gari da bakon ido.

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan yadda abubuwa ke tsada saboda Ramadan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel