Asiri ya tonu : Alkaliyar kotun zabe ta tabbatar da cewa ta amsa cinhanci daga hannun Dino Melaye

Asiri ya tonu : Alkaliyar kotun zabe ta tabbatar da cewa ta amsa cinhanci daga hannun Dino Melaye

Alkaliyar babban kotun jihar Cross River, Akon Ikpeme, wacce aka saki maganar odiyo da jaridar Sahara reporters ta saki cewa ta amsa cin hanci hannun Sanata Dino Melaye ta tabbatar da gaskiyan labarin.

A maganar wayan tarhon, an samu cewa Jastis Akon Ikpeme na fadawa Dino Melaye ya biya ta cin hancin a dalar Amurka.

Jastis Akon Ikpeme ta bayyanawa wani a fadar shugaban kasa cewa lallai Dino Melaye yayi kokarin ganawa da ita lokacin da asiri ya tonu cewa ta musanta yin maganan inda yayi mata alkawarin cewa zai goge maganar a asusun kamfanin sadarwan MTN da jami’an tsaro.

Asiri ya tonu : Alkaliyar kotun zabe ta tabbatar da cewa ta amsa cinhanci daga hannun Dino Melaye

Asiri ya tonu : Alkaliyar kotun zabe ta tabbatar da cewa ta amsa cinhanci daga hannun Dino Melaye

Bayan amsan kudi, Dino Melaye yayi mata alkawarin cewa zai samawa diyar Jastis Akon Ikpeme aiki a ma’aikatar lafiyan jihar Cross River. Duk da cewa bata bayyana adadin kudin da ta karba ba, ta tabbatar da cewa ta amsa.

KU KARANTA: Smart Adeyemi yace a binciki Dino Melaye da kyau

Baya ga haka, lauyoyi sun tabbatar da cewa lallai muryan alkaliyar kotun ne aka saurara a maganar rediyon.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel