Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki zai aurar da yarsa

- Yarinyar, Tosin, mai shekaru 25 zata amarce da saurayinta nan bada dadewa ba

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da matarsa sun fara shirye shiryen gudanar da bikin auren babban yarsu Tosin Saraki, inji jaridar Daily Trust.

Mahaifiyar Yarinyar, kuma uwargidar Saraki Toyin Saraki ce ta bayyaka hakan a shafin ta na Instagram inda ta nuna farin cikinta da sanya ranar auren yarta.

KU KARANTA: Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

Toyin tace “Ina matukar farin cikin sanya ranar auren babbar diyata, nan bada dadewa ba za mu aurar da ita ga saurayinta.” Sa’annan ta kara da bayyana godiyarsu ga masu yi musu fatan alkhairi.

Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

Saraki da Matarsa

Ko a kwanakin baya, majiyar NAIJ.com ta ruwaito a yayin bikin kaddamar da shirin allurer rigakafi sai da uwargidar Saraki tace ta dade tana hidimar uwa, a yanzu burinta ta fara hidimar kaka.

Biki bidiri: Sanata Saraki zai aurar da babbar Ýarsa

Yarinyar Saraki, Tosin Saraki

Sai dai Toyin tace ba zasu bayyana sauran bayanan bikin ba har sai lokaci yayi, amma duk da haka, jama’a basu fasa cigaba da yi musu addu’o’in fatan alheri ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya auren kabila?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel