Wani Fasto a Kaduna ya ciyar da Musulmai 500 a watan Ramadana

Wani Fasto a Kaduna ya ciyar da Musulmai 500 a watan Ramadana

- Fasto a Kaduna ya ciyar da jama'a Musulmai abinci shan ruwa

- Sama da Musulmai 500 ne suka amfana da wannan tagomashi

Wani Faston babban coci a Kaduna, Fasto Yohana Buru ya ciyar da sama da Musulmai 500 abincin shan ruwa tun bayan fara Azumin watan Ramadan.

Fasto Buru ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labaru, NAN, a ranar Litinin 5 ga watan Yuni, inda yace cocin nasa na baiwa gayiyayyu da talakawa tallafin ne domin samun sauki radadin ralauci.

KU KARANTA: Ban ji daɗin yadda Pantami yayi min tayin shiga Musulunci ba – Inji Solomon Dalung

Faston yace “Cocinmu ta saba shirya irin wanna tallafi domin kawo kyakkyawan fahimta tsakanin mabiya addinin Musulunci dana Kirista,Ya zama wajibi akan mu mu taimaki junanmu a wanna watan sakamakon tsadar kayan masarufi da ake fama da shi.”

Wani Fasto a Kaduna ya ciyar da Musulmai 500 a watan Ramadana

Fasto Buru

Buru yace sun saba bada irin wanna tallafi, ind ayace ko a Azumin bara sai da suka ciyar da Musulmai 1000 a watan Ramadan, sa’annan ya koka kan yadda yan kasuwa ke wasa wukarsu a watan Ramadan ba tare da duba ga koyarwan addinin Musulunci ba.

Shima wani daga cikin wadanda suka amfana da rabon, Malam Isa Wambai shugaba makafi na jihar Kaduna ya gode ma Fasto Buru kan taimakon dayake musu, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda direban Fasto ya musulunta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel