Ba zamu taba yarda da yunkurin kara farashin kudin mai ba - NUPENG

Ba zamu taba yarda da yunkurin kara farashin kudin mai ba - NUPENG

Kungiyar gamayar ma’aikatan kamfanin man fetur da iskar gas wato Nigerian Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) ta lashi takobin cewa ba zata taba lamuntan yunkurin kara farashin kudin man fetur ba.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran najeriya NAN, a Legas, Alhaji Tokunbo Korodo, shugaban kungiyar ta NUPENG reshen kudu maso yammacin Najeriya, ya ce bai kamata a gabatar da kudirin ba, a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin hali na matsin rayuwa, dan haka kungiyar hadi da dukkanin reshunan na kwadago, ba zasu taba amincewa da wannan yunkuri ba.

Kamfanin dillancin labaran najeriya NAN, ta bada rahoton cewa shugaban kungiyar NUPENG reshen kudu maso yamma, Alhaji Tokunbo Korodo, ya bayyana rashin kamatan gabatar da irin wannan kuduri a wata lokaci da yan Najeriya ke cikin halin kakanikaye, saboda haka kungiyar tana magana da babban murya cewa hakan ba zai yiwu ba.

Ba zamu taba yarda da yunkurin kara farashin kudin mai ba - NUPENG

Ba zamu taba yarda da yunkurin kara farashin kudin mai ba - NUPENG

Karkashin sakon, wanda Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ya gabatarwa zauren majalisar dattijan a ranar Juma’ar da ta gabata, za’a dinga biyan harajin naira biyar, kan kowace litar, za’a kuma yi amfani da harajin ne, wajen gina manyan hanyoyi a sassan kasar.

KU KARANTA: Reno Omokri ya soki shugaban kasa Buhari

Kwamitin majalisar dattawan Najeriya karkashin jagorancin Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta gabatar da wata jawabi zauren majalisar dattawan a ranar Juma’ar 2 ga watan Yuni cewa za’a rika biyan harajin naira biyar, kan kowace litar mai , domin kuma yi amfani dashi gina manyan hanyoyi a sassan kasar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel