'Dalilin cire sunan gwamna Bello daga Rajistar INEC'

'Dalilin cire sunan gwamna Bello daga Rajistar INEC'

- Gwamna Bello yace fatalwarsa ce tayi rajista ta biyu

- INEC hukumar zabe ta ce ba zata lamunci shugabanni su koya wa al'umma aringizon kuri'u ba

- An ma cire duk sunan gwamnan daga jaddawalin zabe

A dambarwa ta kwana-kwanan nan da ake jiyo wa a siyasar jihar Kogi, shugabannin hukumar INEC sun cire sunan gwamna Bello daga rajista gaba daya. Shi kuwa ma gwamna yace sai dai fatalwarsa ce tayi rajistar ba dai shi ba.

A baya dai gwamna Bello ya taba yi rajista da INEC a Abuja, kwatsam a makon sh/jiya kuma sai gashi yana rajista a karo na biyu. Shu kuwa yace sai dai in fatalwarsa ce, domin shi a lokacin yana Dubai ma.

KU KARANTA KUMA: Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci - Fadar Shugaban Kasa

'Dalilin cire sunan gwamna Bello daga Rajistar INEC'

'Dalilin cire sunan gwamna Bello daga Rajistar INEC'

Gwamnan Kogin dai ya sha suka daga INEC, jam'iyyarsa da ma na cikin gida irinsu Dino Melaye, wanda yace yayi murabus kawai.

Siyasar Kogin dai abun dubawa ce domin wanda ya fara cin zaben Abubakar Audu ya rasu kafin a gama zabe, sai magajinsa kuma yaki yarda ya karbi mataimaki, jam'iyya kuwa ta dauko shi Bello ta bashi a fala.

Yanzu dai babu wani suna na shugaban jihar kogin a rajista, ku biyo mu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel