Na sayar da yara 20 kowanne a farashin N150,000 zuwa N200,000 - Chinaza Onwuasoanya

Na sayar da yara 20 kowanne a farashin N150,000 zuwa N200,000 - Chinaza Onwuasoanya

Dubun wata mata mai suna Chinaza Onwuasoanya, ya cika yayinda jami’an yan sandan SARS sukayi ram da ita a jihar Anambra akan laifin satan yara.

Chinaza Onwuasoanya,ta fara wannan aiki ne lokacinda ta sayar da diyarta ga wata wata mai suna Goddness a kudi N150,000. Kawai sai ya zama sana’a a gareta.

Chinaza Onwuasoanya,ta bayyanawa yan jarida cewa, “ Na fara sana’ar sayar da yara ne shekaru 2 da suka gabata. Na sayar da yara 20 maza da mata ga Madam Goodness mai gidan marayu. Tana biyana N150,000 zuwa N200,000 akan kowani yaro ko yarinya.

Na fara haduwa da ita ne lokacin da nayi juna biyu kuma na haifi diya mace a 4 ga oktoban 2013. Bayan na haihu, sai wata abokiyata ta hada ni da Goodness. Na kai mata diyata kuma ta bani N150,000 domin kula da kaina.

“Bayan wannan lokaci, sai na fara garkuwa da yaran mutane masu dawowa daga makaranta ko kuma a kan titi. Sannan in kaiwa Madam Goodness ta bani N150,000 zuwa N200,000.

Na sayar da yara 20 kowanne a farashin N150,000 zuwa N200,000 - Chinaza Onwuasoanya

Na sayar da yara 20 kowanne a farashin N150,000 zuwa N200,000 - Chinaza Onwuasoanya

“Amma a ranan 1 ga watan Mayu, 2017 ne aka kamani lokacin da na sace jarirai yan biyu a Onitsha na kaisu gidana. Kawai ashe mahaifin na biye da ni inda ya kira yan sanda sukayi ram da ni."

KU KARANTA: Karin kudin mai zalunci ne - yan adawa

Al’amarin ba nan ta kare ba, Onwuasoanya ta bayyana cewa tana musharaka da yan fashi a jihar Anambra wadanda suka kashe wasu yan sanda 2 -Shuaibu Usman and Julius Matthew- a ranan 29 ga watan Febrairu.

Kana ta taimakawa hukumar SARS wajen kama abokan aikinta 3 amma sauran 6 suka arce.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel