'Abubuwa da suka sa Buhari ba zayyi Nasara ba

'Abubuwa da suka sa Buhari ba zayyi Nasara ba

- Ya kwatanta Buhari da wanda bai yi nasara a fagen kasuwanci ba. Inda ya ce Shugaban Amurka yafi shi

- Reno Omokri Pastor ne da ya ke zaune a Amurka, kuma tsohon mai taimakawa shugaba Jonathan

- Yace Buhari bai iya mulki ba kuma ko a baya ma bai iya kasuwanci ba

Tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce in dai ana so a gane yadda shugaba Buhari ke salon mulkinsa sai an duba yadda yake kasuwanci a baya. A cewarsa ai harkar kasuwancin shugaban rugujewa tayi, shi yasa yana hawa mulki shima tattalin arzikin kasar ya ruguje.

Ya kwatanta Buhari da shugaban Amurka inda yace dayan hamshakin dan kasuwa ne, shine ma yasa ya fara diban ma'aikata kwanaki kadan bayan hawansa mulki.

"Juma'ar da zata yi kyau tun laraba ake fara gane ta, dubi yadda shugaban Amurka ke samun nasara cikin kwanaki kadan da hawansa mulki, shiko Buhari shiru kake ji shekaru biyu kenan", ya wallafa a shafinsa na facebook.

'Abubuwa da suka sa Buhari ba zayyi Nasara ba

'Abubuwa da suka sa Buhari ba zayyi Nasara ba

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kuka da kansu su kula da wa zasu zaba a zabukan 2019 masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

Ba'a dai san ko yana share ma uban gidansa hanya bane don ya yi takara a zabe mai zuwa ba. Amma dai har yanzu bai dawo Najeriya da zama ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel