Sukar da ake wa Buhari da Sani Bello ba daidai ba ne, sun yi rawar gani – Inji kungiyar kiristocin Najeriya

Sukar da ake wa Buhari da Sani Bello ba daidai ba ne, sun yi rawar gani – Inji kungiyar kiristocin Najeriya

- Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta yaba wa gwamnatin shugaba Buhari da kuma gwamnan jihar Neja cewa sun yi rawar ganin

- Kungiyar ta shawarci shugabannin da yin adalci tsakanin al’umma a wajen bikin nuna godiya da cika shekaru biyu da gwamna Abubakar Sani Bello ya yi a ofis

- Shugaban CAN, Rev Mathias Echioda ya yi addu’an zaman lafiya da kuma hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya

Duk da kukan da wasu ‘yan Najeriya a kan gazawar da jama'iyyar mai mulki APC karkashin jagorancin shugaban kasar Muhammadu Buhari, kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN ta soki lamirin masu sukar gwamnati mai ci, kungiyar ta ce, gwamnatin nan ta yi rawar gani a fannoni daban daban.

NAIJ.com ta ruwaito cewa a lokacin da yake magana a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuli a wani sakon mai lakabi: "Jagoranci da adalci," na taron bikin nuna godiya da kuma yabo da cika shekaru biyu a matsayin gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello wanda aka yi a Minna babban birnin jihar. Shugaban CAN, Rev Mathias Echioda, ya shawarci gwamnati da ta nisanta wasu munafikan ‘yan siyasa.

A cewar Echioda: "Ba daidai ba ne a ce wai wannan gwamnatin ba ta aiki. Duk wanda ke sukar gwamnati ya kamata su iya daidaita zargin na su.’’

Sukar da ake wa Buhari da Sani Bello ba daidai ba ne, sun yi rawar gani – Inji kungiyar kiristocin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na saukowa daga jirgin sama a lokacin da ya ziyarci kasar Amurka

Ya kara da cewa: ” Idan aka tambaye ni cewa ko wannan gwamnatin tarayya a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja sun yi aiki? Amsa na shine, duk sun yi aiki.”

KU KARANTA: Bayan tafiyar Buhari, Osinbajo yayi bayani game da rashin adalci wajen nade-naden sa

Fastocin sun yi addu’a inda suka roka wa shugaban kasar Muhammadu Buhari samu lafiya, sun kuma yi addu’an zaman lafiya da hadin kai a Najeriya, da jihohi, da kuma kananan hukumomi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali abubuwan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a cikin shekaru biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel