Bayan tafiyar Buhari, Osinbajo yayi bayani game da rashin adalci wajen nade-naden sa

Bayan tafiyar Buhari, Osinbajo yayi bayani game da rashin adalci wajen nade-naden sa

- Mukaddashin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo a jiya ya bayyana cewa zargin da ake yi masa da yana yin son kai wajen nade-naden sa abun kunya ne da kuma dariya.

- Osinbajo ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakiyar sa ta musamman a harkokin shari'a mai suna Dr. Bilkisu Saidu wadda tayi kaca-kaca da wani Isma'il Farouk game da zargin sa ga mataimakin shugaban kasar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa an dai tafka wannan zazzafar muhawarar ce a wani shirin safe na gidan BBC Hausa a tsakanin mutanen biyu inda Dr. Bilkisu tace abunda mutane basu gane ba shine mafiya yawan masu aiki a ofishin mataimakin shugaban kasar yan arewa ne kuma musulmai.

A kwanakin nan dai, wata ƙasida da wani dan arewacin kasar ya rubuta kan mukaddashin shugaban kasa na tayar da kura a fagen siyasar kasar.

Bayan tafiyar Buhari, Osinbajo yayi bayani game da rashin adalci wajen nade-naden sa

Bayan tafiyar Buhari, Osinbajo yayi bayani game da rashin adalci wajen nade-naden sa

A cikin kasidar marubucin wanda ya kira kansa Dr. Ismaila Faruk daga jihar Zamfara, ya zargi Farfesa Yemi Osinbajo da nuna banbamci wajen nade naden mukamai.

Marubucin ya yi zargin cewa mukaddashin shugaban kasar na amfani da damar da ya samu wajen nada 'yan kabilarsa ta yarbawa da kuma mabiya majami'ar sa kan manyan mukamai.

Haka kuma murubucin ya ce hakan ya saba wa tanade tanaden kudin tsarin mulki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel