Harin ta'addanci: An kama mutum 12 kan harin London

Harin ta'addanci: An kama mutum 12 kan harin London

- Yan sanda sun kama mutum 12 bayan harin birnin Landan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai ya kuma jikkata wasu 48.

- An kama mutanen ne a garin Barking da ke gabashin Landan bayan wani samame da 'yan sandan suka kai gidan daya daga ciki mahara ukun da suka kai harin.

Wata farar mota ce ta ture wadansu mutane da suke tafiya a ƙafa a kan gadar birnin Landan da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa daga nan ne sai wasu mutum uku suka fito daga motar kuma suka fara daɓawa mutane wuƙa a kusa da kasuwar Borough Market. Sai dai 'yan sanda sun harbe su bayan mintuna kadan.

Harin ta'addanci: An kama mutum 12 kan harin London

Harin ta'addanci: An kama mutum 12 kan harin London

Yayin da take Allah-wadai da harin, Farai Ministar Birtaniya ta ce "lokaci ya yi da za mu ce ya isa haka"

Har ila yau, an gano wasu abubuwan fashewa a wani gida da 'yan sanda suka kai samame a garin Barking ranar Lahadi da safe.

Ɗaya daga cikin maharan da aka kashe ya kwashe shekara uku a gidan kuma yana da mata da 'ya'ya biyu, kamar yadda maƙwabtarsa suka bayyana.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel