Zaben 2019: Yankin kudu maso gabas ba zatayi zabe ba har sai an shirya zaben raba gardama - MASSOB

Zaben 2019: Yankin kudu maso gabas ba zatayi zabe ba har sai an shirya zaben raba gardama - MASSOB

-Gabanin zaben 2019, an fara maganganun tayar da kura musamman yankin kabilar Igbo

Kungiyar fafutukar neman yancin Biafra wato Movement for Actualization of Sovereign State of Biafra (MASSOB) tace babu zaben da za’a gudanar a yankin kudu maso yamma da wasu sassan jihar Kogi da Benue a shekarar 2019 har sai idan gwamnatin tarayya ta shirya zaben raba gardama a yankin Biafra.

Game da cewar kakakin kungiyar, Samuel Edeson, kungiyar tace wasu sassan jihar Kogi sa Benue ma na tattaunawa da MASSOB domin zama cikin yankin Biafra.

Jawabin tace: “ MASSOB na bayar da wa’adin watanni 6 ga gwamnatin tarayya ta gudanar da zaben raba gardama a kasar bIafra ko kuma babu wani zaben da za’a gudanar a yankin kudu maso gabas da wasu sassan jihar Kogi da Benue.

“MASSOB, IPOB, da wasu kungiyoyin yakin neman Biafra zasu tara mutane akan hana zaben kasa a 2019 a dukkan yankin Biafra idan har gwamnatin tarayya taki gudanar da zaben raba gardama domin Biafra ta fita daga Najeriya.

Zaben 2019: Yankin kudu maso gabas ba zatayi zabe ba har sai an shirya zaben raba gardama - MASSOB

Zaben 2019: Yankin kudu maso gabas ba zatayi zabe ba har sai an shirya zaben raba gardama - MASSOB

“Ba zamu takurawa kowa ba, har ma’aikatan zaben; zasu gudanar da ayyukansu amma ba zasu ga kowa ba. babu dan Biafran da zai fito zabe ranan.”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Luwadi ke karuwa a Najeriya

“Idan mutum ya zabi zama a gida, ba zaku tilastashi ya fita yayi zabe ba. mun gaji da Najeriya, babu irin garambawul din da zai hana mu yakin neman Biafra.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel