Kocin Arsenal Arsene Wenger yana zawarcin shahararren dan wasa Riyad Mahrez

Kocin Arsenal Arsene Wenger yana zawarcin shahararren dan wasa Riyad Mahrez

- Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana zawarcin ɗan wasan gaban Leicester City Riyad Mahrez, sai dai ba a fara maganar hakan ba a hukumance.

- Dan wasan mai shekara 26 ya sanya hannu a kan sabon kwantiragi da kulob din Leicester City a watan Agustan bara, amma daga bisani an bukaci ya ƙara gaba.

Mahrez ya taka muhimmiyrar rawa yayin da Leicester City ta lashe Kofin Firimiyar kakar bara, amma a kakar bana sun kammala gasar ne a mataki na 12.

Yayin da aka tambayi Wenger ko sun fara zawarcinsa a hukumance? Sai ya ce "a'a, tukuna. Za mu iya nemansa kuma za mu iya ƙin nemansa," in ji shi.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Mahrez ya koma Leicester City ne daga kulob din Le Havre na kasar Faransa a shekarar 2014 a kan fam dubu 400 kuma a shekarar 2016 ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar gasar Ingila.

Kocin Arsenal Arsene Wenger yana zawarcin shahararren dan wasa Riyad Mahrez

Kocin Arsenal Arsene Wenger yana zawarcin shahararren dan wasa Riyad Mahrez

"Mahrez ya taka muhimmiyar rawa a Leicester lokacin da suka lashe Gasar Firimiya, kamar kowane dan wasan kulob din," in ji Wenger.

Ya ci gaba da cewa "Kakar bana ta sha bamban da ta bara, amma hakan ba yana nuna wata gazawa ba ne daga ɓangaren dan wasan."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel