Zigidir! Shugaban jam’iyyar PDP da mutane 25,000 sun koma APC a wannan jihar ta Arewa

Zigidir! Shugaban jam’iyyar PDP da mutane 25,000 sun koma APC a wannan jihar ta Arewa

- Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da wadansu magoya bayan jam’iyyar 25,000 ne suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC.

- Shugaban jam’iyyar Bello Doya ne ya jagoranci masu canza shekar.

Gwamnan jihar Abubakar Bagudu da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar daga kananan hukumomi 21 ne suka karbe su a wata kwarya-kwaryar buki da akayi a Birnin Kebbi.

A jawabinsa gwamnan jihar yayi maraba da da su sannan yace jam’iyyar APC za ta yi aiki da su kamar kowani dan jam’iyyar.

Zigidir! Shugaban jam’iyyar PDP da mutane 25,000 sun koma APC a wannan jihar ta Arewa

Zigidir! Shugaban jam’iyyar PDP da mutane 25,000 sun koma APC a wannan jihar ta Arewa

NAIJ.com ta samu labarin cewa mai magana da yawun masu canza shekar Isah Argungu ya ce gaba dayansu sun canza sheka ne zuwa jam’iyyar APC saboda kyawawan aiyukan da gwamnatin jihar da na kasa ke yi wa mutanen da suka zabe su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel