Biafra: Ya kamata Buhari ya dau mataki tsattsaura kan IPOB da MASSOB – Ango Abdullahi

Biafra: Ya kamata Buhari ya dau mataki tsattsaura kan IPOB da MASSOB – Ango Abdullahi

Kakakin kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, yayo kir ga gwamnatin tarayya ta dau mataki kan duk kungiyar da zata tayar da kura a Najeriya da suna son fita daga kasa.

Yace a tarihi, yan kabilar Igbo ne suka fara kaiwa Najeriya hari karkashin shugabansu, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, wanda yayi kokarin cin Najeriya,

Abdullahi yace wannan sabon shirin neman yancin ba wani abu bane face siyasa kawai na kasa.

Toh, ya kamata mu lura da cewa sabon fafutukan neman fita daga Najeriya siyasa ce. Ba wani abu bane face siyasan da ake bugawa a Najeriya tun lokacin da muka samu yanci.”

“Siyasa ce ta sa aka fara neman yancin Biafra a Najeriya. Son shugabanci ne ya kawo ta jamhuriyya ta farko wanda ya sabbaba kisa shugabannin farko da kuma tashin Ojukwu.”

Biafra: Ya kamata Buhari ya dau mataki tsattsaura kan IPOB da MASSOB – Ango Abdullahi

Biafra: Ya kamata Buhari ya dau mataki tsattsaura kan IPOB da MASSOB – Ango Abdullahi

“Haka kawai, Ojukwu wanda yayi tunanin cewa an kai hari ga inyamurai sabanin hakikanin zance na cewa Inyamurai ne ke kokarin kawo hari Najeria. A sani cewa Ojukwu tare da wasu manyan Igbo sunyi tunanin kwace Najeriya ne.”

“Saboda haka, wannan abu mai suna Biafra na tushen juyin mulkin 1966 kuma ina bayyana cewa idan mutanen ne na bukatan fita bayan shekaru 50 na yakin basasa, toh gaskiya ya kamata mu zauna muyi tunanin abinda muke bukata a matsayin tarayya.”

KU KARANTA: Sarauniyar kyau ta karbi musulunci

“Kan daukan mataki kan wannan fafutukan neman Biafra, gwamnatin tarayya ta bi kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ta dakile duk wani kungiya da ke kokarin tayar da hankali jama’a da kowani manufa.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel