Shiriya daga Allah: Sarauniyar kyau ta Musulunta

Shiriya daga Allah: Sarauniyar kyau ta Musulunta

- Wata Sarauniyar kyau yar kasar Czech Republic data samu haske ta Musulunta

- Budurwar mai suna Marketa Korinkova ta koma Maryam

Wata kamfanin jaridar kasar Birtaniya ta ruwaito labarin wata Sarauniyar kyau yar kasar Czech Republic data samu haske ta Musulunta, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Budurwar mai suna Marketa Korinkova wadda a baya Kirista ce ta gane hasken Musulunci ne yayin da take karatu a jami’ar Charles dake Prague shekaru 3 da suka gabata.

KU KARANTA: Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

A yanzu haka Marketa ta koma zama a kasar Dubai da zama, kuma ta sauya sunanta zuwa Maryam, inda tace ta gamsu da zaman kasar Dubai, don ta kara samun daman fahimtar addini.

Shiriya daga Allah: Sarauniyar kyau ta Musulunta

Musulma

Maryam tace abinda tafi kauna a kasar Dubai shine kwanciyar hankali da saukin rayuwa, ba wai wani kyale kyalen gidaje ba.

Maryam tace bata ganin ana cin zarafin Musulmai mata a Musulunci, inda tace sama da shekaru 1400 da suka gabata musulunci ya tanadar da hakkin mata, tare da kuma rashin bautar dasu, sa’annan Musulunci ya baiwa mata damar shigar harkar mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel