Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

- Ministan bayanai da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammad ya bayyana haske dalilan da ya sa yawancin ‘yan Najeriya ke daukar sa a matsayin makaryaci

- Ya ce dalili na farko shine alakanta shi da ‘yan Najeriya ke yi da bangaren adawa

- Ya bayyana cewa ya sha kalubalantan mutane da su nuna masa karya guda daya da ya yi, kuma ba sa iya yin hakan

Ministan bayanai da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammad ya bayyana haske kan dalilan da ya sa yawancin ‘yan Najeriya ke daukar sa a matsayin makaryaci.

A wata hira da aka yi da shi a shirin “Osasu show” na gidan talabijin din AIT, ministan ya ce dalili na farko shine alakanta shi da ‘yan Najeriya ke yi da bangaren adawa, inda ya shafe shekaru 10 kafin su samu kafa gwamnati mai ci.

KU KARANTA KUMA: Gada ya fadi a jihar Niger (HOTUNA)Gada ya fadi a jihar Niger (HOTUNA)

Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

Alhaji Lai Mohammad ya bayyana haske dalilan da ya sa yawancin ‘yan Najeriya ke daukar sa a matsayin makaryaci

Ya ce wannan ne ya sa ake yawan kwatanta abubuwan da ya fada a lokacin da yake a bangaren adawa da kuma abubuwan da yake fada a yanzu.

NAIJ.com ta tattaro inda ya bayyana cewa ya sha kalubalantan mutane da su nuna masa karya guda daya da ya yi, kuma ba sa iya yin hakan.

A cewar shi, duk wadanda ke cewa ya na karya sai dai su fadi haka akan san zuciyar su, ba don saboda suna da wasu kwakkwaran hujja ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku wannan bidiyo mai ban tausayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel