YANZU YANZU: Tsohon ministan lafiyar Najeriya Babatunde Osotimehin ya rasu

YANZU YANZU: Tsohon ministan lafiyar Najeriya Babatunde Osotimehin ya rasu

- Wani tsohon ministan lafiyar Najeriya, Babatunde Osotimehin ya mutu

- Har mutuwar sa, Osotimehin ya kasance babban darakta a hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA)

- Ya kuma kasance tsohon shugaban makarantar koyon likitanci, jami’ar Ibadan

Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya na Najeriya kuma babban darakta a hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA), Farfesa Babatunde Osotimehin, rasuwa.

NAIJ.com ta tattaro cewa an haifi Osotimehin wanda aka haifa a ranar 6 ga watan Fabrairun shekara ta 1949 ya kasance tsohon shugaban makarantar koyon likitanci a jami’ar Ibadan.

KU KARANTA KUMA: Gada ya fadi a jihar Niger (HOTUNA)

Marigayin ya mutu yana da shekaru 68 a duniya.

YANZU YANZU: Tsohon ministan lafiyar Nigeria Babatunde Osotimehin ya rasu

Mabatunde Osotimehin

Premium Times ta rahoto cewa majiyoyi kusa da tsohon ministan sun bayyana cewa ya mutu sassafiyar ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.

Sanarwar ba ta bayyana sababin mutuwar tasa ba, amma dai ta ce iyalansa sun "nuna godiya ga Allah kan tsawon rai" da kuma nasarorin da ya bashi a rayuwarsa ta duniya.

Ya rike mukamin ministan lafiya a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010.

Sai a nan gaba ne za a bayyana lokaci da kuma inda za a binne marigayin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ministan sufuri Rotimi Ameachi ya fadi nasarorin gwamnatin Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel