Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

- Wani mutum ya kima ma yarsa ciki, ta haifi mace

- Mutumin yayi yunkurin hallaka jaririyar da aka haifa ta hanyar jefa ta rijiya

Rahotanni daga jihar Bauchi na sun bayyana cewar wani magidanci da ake zargin da dibga ma yarinyar cikinsa ciki, kuma har ya jefa jaririn cikin rijiya, kamar yadda wani ma’abocin Facebook, Bashir El-Bash ya bayyana.

Mutumin mai suna Abdulkadir Muhammad mai shekaru 55, mazaunin garin Gamawa ne na jihar Bauchi ya shiga hannun jami'an tsaro a dalilin tuhumar da ake yi masa na yi wa 'yar cikin sa mai shekaru 20 mai suna Dije ciki.

KU KARANTA: Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci

Dije Abdulkadir ta tabbatar da saduwa da mahaifin nata, sa’annan kuma ta tabbatar da yunkurin kashe yar data haifa, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta kalato.

Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

Abdulkadir

Kwamishinan Yansandan jihar Bauchi Garba Umar ya bayyana haka, inda ya bayyana zargin da ake tuhumar mutumin, tare da hada baki wajen yunkurin hallaka jaririyar da aka haifa ta hanyar jefa ta a cikin rijiya.

Uba ya ɗibga ma Ýar’sa ciki, ya jefar da jaririyar cikin rijiya

Dije da jaririyarta

DPO Yansandan Gamawa ne ya fara samun koke daga makwabtan mutumin wadanda suka kawo karar abinda ya faru domin a ceto rayuwar jaririyar da mutumin ya jefa ta cikin rijiyar.

Nan bada dadewa ba za’a tura Dije da mahaifinta Malam Abdulkadir gaban kuliya manta sabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene alakar Yansanda da jama'a?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel