Yara na nuna sha’awar komawa karatu a Diffa – Inji UNICEF

Yara na nuna sha’awar komawa karatu a Diffa – Inji UNICEF

- Hukumar UNICEF ta ce yara da ke Diffa a kasar Nijar na nuna sha’awar komawa karatun boko

- Daraktar shiyar, Marie-pierre Poirier ta ce yana da muhimmanci a tura yaran zuwa makaranta

- Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka makarantu kusan 30 ke rufe a Diffa

Hukumar UNICEF da ke kula da ilimin yara kanana ta sake jaddada muhimmancin tura yara zuwa makaranta a yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, da ya yi fama da hare haren kungiyar Book Haram kusan shekaru biyu.

Daraktar shiyar da ke kula da kasashen yammaci da tsakiyar Afirka Marie-pierre Poirier ta bayyana haka a ziyarar da ta kai Diffa, inda ta bayyana muhimmancin tura yaran zuwa makaranta.

Alkalumma sun nuna cewar makarantu 166 aka rufe a kasar Nijar, kafin gwamnatin kasar da hukumar UNICEF su sake bude makarantu 99 bara.

Yara na nuna sha’awar komawa karatu a Diffa – Inji UNICEF

Yara a yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar

KU KARANTA: Lissafi ya nuna cewa Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki – Ministan Kudi

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka makarantu kusan 30 ke rufe a Diffa da kusa da Kogin Komadougou da ke iyaka da Jihar Yobe.

Yara da malamai na kauracewa makarantu saboda barazanar hare haren ‘Yan Boko Haram. Amma babbar jami’ar UNICEF Marie-Pierre ta ce a ziyarar da ta kai a yankin yara da dama sun nuna sha’awar komawa karatu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel