'Karin N5 kan kudin man fetur zalunci ne'

'Karin N5 kan kudin man fetur zalunci ne'

- Ana kishin kishin za'a dora N5 kan farashin mai don samar da kudin yin gyara da sabbin tutina

- Hadakar jam'iyyun adawa ta CNPP sun ce hakan zalunci ne da kuntata wa talaka

- A majalisar dattijai aka kawo batun, karkashi kwamitin ayyuka na Sanata Kabiru Gaya

Ana wata sai ga wata, kwatsam sai talakawa suka ji wai ana kokarin a kara kudin mai, bayan irin kunci na tattalin arziki da suke ciki, karin kudi har naira biyar, wanda a cewar masu son karin, Kwamitin majalisa na Sanatan Kano ta kudu Kabiru Gaya ke cewa kudin zai taimaka wajen karo kudi don inganta tituna, dama fidda sabbi, tunda gwamnati ta kasa kawo wasu hanyoyin na samun karin kudi.

Hadakar jam'iyya dai ta adawa, CNPP, tace wannan zalunci ne, domin in ba rage kudin mai ba babu dalilin a kara shi a irin wannan marra da ake ciki.

Cif Willy Ezwugu ne ya fitar da sanarwas, ya kuma gargadi gwamnati da kada ta kuskura ta latsa talakkan Najeriya da raini.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

'Karin N5 kan kudin man fetur zalunci ne'

'Karin N5 kan kudin man fetur zalunci ne'

"Bincikenmu ya nuna cewa kwamitin majalisar da ya bada kudirin na yadda za'a samar da kudaden 2017 don ayyuka ne ya bada shawarar, to ahir!" inji shi.

"Mu a zatonmu ma za'a rage yawan farashin ne, duba da yadda ake shan bakar wahala a kasar nan, kwatsam sai muka ji kari ne ma suke so suyi, wannan ai baza ta abu ba", ya kara da cewa.

NAIJ.com ta tuna cewa a shekarun baya an sami lokuta daban daban da ake kara kudin mai kuma hakan take wucewa domin in dai farashin mai ya daga baya dawowa yadda yake da, duk yaji da zafi. Shiko farashin mai, tafe yake da sauran farashi na kayan masarufi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wani bidiyo mai ban tausayi da NAIJ.com ta kawo maku

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel