Tuwo na mai na: Jam’iyyar APC ta lashe kafatanin kujerun ƙananan hukumomi

Tuwo na mai na: Jam’iyyar APC ta lashe kafatanin kujerun ƙananan hukumomi

- Jam’iyyar APC ta lashe kafatanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Benuwe

- Jam’iyyar APC ta lashe zabukan kujerun kansiloli 182

Jam’iyyar APC a jihar Benuwe ta lashe zabukan kananan hukumomin daya gudana a ranar Lahadin data gabata, 4 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwwaito.

Jam’iyyar ta APC ta lashe zabukan ne a kafatanin kananan hukumomi 23 dake jihar Benuwe, kamar yadda shugaban hukumar shirya zabuka mai zaman kanta na jihar , Dakta John Tsuwa ya sanar yayin bayyana sakamakon zaben.

KU KARANTA: Solomon Dalung ya halarci Tafsirin Sheikh Pantami

Shugaban hukumar, Dakta Tsuwa ya bayyana jam’iyyar APC ta lashe kananan kujerun kansiloli 182, inda sauran jam’iyyun suka lashe sauran kujeru guda 94.

Tuwo na mai na: Jam’iyyar APC ta lashe kafatanin kujerun ƙananan hukumomi

Jam’iyyar APC

Tsuwa ya kara da cewa jam’iyyun siyasa takwas ne suka fafata a zabukan, inda aka yi amfani da rumfunan zabe 3,691, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Sai dai sakamakon takkadamar da jam’iyyar PDP ke fuskanta na shugabanci tsakanin Ali Modu Sheriff da Ahmed Makarfi, hakan ya haramta ma tsagin Ahmed Makarfi shiga zaben.

Daga karshe, Tsuwa ya bayyana gamsuwarsa da zabukan, musamman yadda suka gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, inda ya bayyana cewar ba’a taba samun zabe sahihi ba kamar wannan a tarihin jihar Benuwe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da gaske Dansanda abokin kowa ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel