'A binciki batun cin hancin Dino Melaye da kyau' - Sanata Smart Adeyemi, wanda Melayen ya kayar

'A binciki batun cin hancin Dino Melaye da kyau' - Sanata Smart Adeyemi, wanda Melayen ya kayar

- Smart Adeyemi ne a kan kujerar Dino Melaye a da, yana jam'iyyar PDP

- Batun sayen kuri'u, sayen alkalai na neman korar Dino Melaye daga majalisa

- Anfi dai ganin Sanata Melaye a matsayin dan-siyasar tasha maras dattako

Sanatan PDP da DIno Melaye ya kwacewa kujera yace da walakin, wai goro a miya, yadda aka yanke hukunce-hukunce a karkashi alkaliya Akon Ikpeme, wadda ake zargi da karbar makudan daloli daga hannun Dino Melaye har sau biyu, kan batun zabensa a 2015 a matsayin Sanata daga jihar Kogi, a karkashin jam'iyyar APC.

A jiya lahadi, tsohon Sanata Smart Adeyemi ya mika kokensa ga jami'an tsaro da shuwagabannin kotu kan lalle su binciki Sanata Melaye wanda ya kayar dashi a zaben da ya gabata, a jam'iyyar APC, shi kuwa har yanzu yana PDP, yace akwai kanshin gaskiya batun anyi masa magudi.

"Wannan murya da aka ji lallai ta Joji mai alkalanci Ikpeme ce, wadda aka jiyo tana cinikin nawa za'a biya ta ta baiwa Melaye gaskiya, wanda Sahara Reporters suka yada, ya kamata a duba",Ya fadi.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ‘Yan Najeriya suka dauke ni makaryaci – Lai Muhammad

'A binciki batun cin hancin Dino Melaye da kyau' - Sanata Smart Adeyemi, wanda Melayen ya kayar

'A binciki batun cin hancin Dino Melaye da kyau' - Sanata Smart Adeyemi, wanda Melayen ya kayar

"Dama dai nayi zargin akwai makarkashiya kan yadda ta bayar da hukunce-hukunce a dukunkune, don haka ina kira da hukumomin 'yansanda, kotu, da 'yansandan farin kaya, su zo su binciki wannan zargi", ya kara da cewa.

Ana dai yamadidin cewa faifan muryar da akayi cinikin kujerarsa da joji mai hukunci ya fita, kuma ma wai ita har ta garzaya fadar shugaban kasa neman mafita.

Shi ko gogan naka Dino Melaye, wanda ake zargin, yaki daukar waya ko amsa tambayoyin 'yan jarida, yayi biris kamar bai damu ba.

NAIJ.com ta tuna cewa a baya ya sha tsallake irin-irin wadannan zarge zarge, da yace siyasa ce kawai ta 'yan bakin gida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel