Harin Boko Haram ya kashe mutane 21 a kusa da Chibok

Harin Boko Haram ya kashe mutane 21 a kusa da Chibok

- Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a kauyukan da ke kusa da garin Chibok

- Harin da yan ta’addan suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar yan fararen hula guda 21

Rahotanni dake zuwa sun nuna ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hare-hare a kauyukan da ke da kusa da garin Chibok da ke jihar Borno, a jiya Lahadi, 4 ga watan Yuni.

Harin da yan ta’addan suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar yan fararen hula guda 21.

A cewar wani mazaunin garin Chibok da aka ambata da suna Chibok Hassan ya bayyana cewa ko kafin harin, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai irin wannan harin a ranar Larabar da ta gabata.

Harin Boko Haram ya kashe mutane 21 a kusa da Chibok

Harin Boko Haram ya kashe mutane 21 a kusa da Chibok

Ya kara da cewa: " ‘yan Boko Haram sun fara yin dirar mikiya a wani kauye mai suna Kaya mai nisan akalla kilomita 27 tsakaninsa da garin Chibok

“Zuwa yanzu babu sauran mutum ko daya a kauyen Kaya sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka kai a kan kauyen Kaya. Mayakan sun shigo ne da yamma haye akan babura, inda da shigarsu kauyen suka budewa mutane wuta”, cewar Hassan.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: An zuba jami’an tsaro 600 a massalatai da cocina a Maiduguri - NSCDC

“Sun kona gidaje da dama wadanda suka yi sa’ar arcewa sun arce sun bar kauyen, yayinda ‘yan ta’addan suka hallaka wadanda suka rage.”

Hassan ya kara da cewa: “Labarin harin na ranar Laraba bai game gari bane sakamakon Kaya karamin kauye ne kuma a cikin daji”.

Kwana biyu kacal bayan wancan hari da aka kai akan kauyen Kaya, mayakan Boko Haram sun sake kai wani harin a kan wani kauye kusa da garin Gumsari inda suka yi sanadiyyar kashe mutane 14.

NAIJ.com ta samu labarin cewa duk wani kokari na a tabbatar da sahihancin wannan labari daga bakin rundunar sojin Najeriya ta bakin kakakin ta, Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya ci tura sakamakon wayarsa da ke a kashe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel