Boko Haram: An zuba jami’an tsaro 600 a massalatai da cocina a Maiduguri - NSCDC

Boko Haram: An zuba jami’an tsaro 600 a massalatai da cocina a Maiduguri - NSCDC

- Hukumar NSCDC, sashin jihar Borno ta tura jami’an tsaro 600 zuwa guraren bauta daban-daban a Maiduguri

- An zuba jami’an tsaron ne domin su zamo kariya ga masu bauta

- Zasu taimaka gurin dakile hare-haren da yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram ke kaiwa guraren bauta, musamman a watan Ramadan

Hukumar NSCDC, sashin jihar Borno ta tura jami’an tsaro 600 zuwa guraren bauta daban-daban a Maiduguri domin ba masu bauta kariya na musamman.

Shugaban hukumar na jihar, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni lokacin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Maiduguri.

Ya bayyana cewa tura jami’an na daga cikin kokari da ake na dakile hare-haren da yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram ke kaiwa guraren bauta, musamman a watan Ramadan.

Boko Haram: An zuba jami’an tsaro 600 a massalatai da cocina a Maiduguri - NSCDC

An zuba jami’an tsaro 600 a massalatai da cocina a Maiduguri saboda hare-haren Boko Haram

Mista Abdullahi ya ce hukumar ta kara karfafa tsaro a guraren kasuwanci, kasuwanni, garajin motoci, guraren shakata da kuma manyan shaguna a babban birnin jihar domin tabbatar da kariya ga al’umma.

KU KARANTA KUMA: Abin Murna: Buhari zai dawo bakin aikinsa nan da sati – Inji Kalu

“Muna rokon al’umman da su taimaki hukumomin tsaro da muhimman bayanai da zai taimake mu gurin dakile duk wani barazana daga kungiyar Boko Haram da sauran tsageru.

“Muna ba dukkanin guraren bauta a yankunan da bamu zuwa jami’an mu ba shawara da su tabbatar wasu mutane na tsaron su yayinda suke sallah.

“Kula da bakin fuska,” Mista Abdullahi ya yi gargadi

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel