Abin Murna: Buhari zai dawo bakin aikinsa nan da sati – Inji Kalu

Abin Murna: Buhari zai dawo bakin aikinsa nan da sati – Inji Kalu

- Orji Uzor Kalu a ranar Lahadi ya ce shugaba Buhari na samu sauki kuma zai dawo Najeriya don ya ci gaba da aikinsa nan da sati daya

- Kalu dai ya ziyarci shugaba Buhari a Landan don ya duba lafiyarsa

- Kalu ya kuma ce abin takaici ne ganin yadda wasu ‘yan Najeriya ke yada karyan jita-jita game da kiwon lafiyar shugaba Buhari maimakon yi masa addu'a

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu sauki sosai a lokacin da ya ziyarce shi a makon da ta gabata a London.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Kalu ya bayyana cewar shugaban kasar zai iya dawo gida kafin ranar 11 ga wannan watan, ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su nizanci yada jita-jita na kiyayya game da kiwon lafiyar shugaban wanda ya ce a halin yanzu ya samu lafiya.

Yayin da yake magana a cikin wata hira a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas, Kalu ya ce abin takaici ne ganin yadda wasu ‘yan Najeriya ke yada karyan jita-jita game da kiwon lafiyar shugaba Buhari maimakon yi masa addu'a samu domin ya koma bakin aikin sa.

Buhari zai dawo bakin aikinsa nan da sati – Inji Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu

Kalu ya ce ya ziyarci birnin Landan ne musamma don ya duba kiwon lafiyar shugaba Buhari. Ya ce: "Na tafi Washington don na ziyarci abokan kasuwanci na kuma daga can na biya Landan don ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu yana murmurewa sosai.”

“Na yi farin ciki yadda na samu shugaba Buhari duk da sakonnin kiyayya da wasu mutane ke yadawa game da shi. Amma kuma ina bakin ciki game da maganganu na kiyyaya da wasu ‘yan Najeriya ke fada game da lafiyar shugaban don na gani wa ido na yadda shugaban kasar yake.”

A wni bangare kuma tsohon gwamnan ya ce ya yabawa shugaba Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa kuma durkushe ‘yan ta’adda Boko Haram.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci mutane da su yi hakuri

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel