Dalilai 3 da yasa ‘yan Najeriya ke tunanin Buhari bai yi komai a gwamnatinsa ba

Dalilai 3 da yasa ‘yan Najeriya ke tunanin Buhari bai yi komai a gwamnatinsa ba

- Dalilai 3 da yasa ‘yan Najeriya ke tunanin Buhari bai yi komai ba a tsawo shekaru 2 akan kujera

- Ra'ayoyin ‘yan Najeriya kan abunda gwamnatin shugaba Buhari ta shuka tsawon shekaru biyu ta bayyana a ranar dimokaradiyya

- Wasu ‘yan Najeriya sun caccaki gwamnatin cewa ta fadi warwas

Tun daga ranar dimokaradiyya ta kasa, mafi yawan al'ummar Najeriya sun bayyana ra'ayoyin kan abunda gwamnatin shugaba Buhari ta shuka tsawon shekaru biyu, sai dai kashi 55 suka ce gwamnatin ta fadi, cewar su babu wani abun azo a gani da gwamnatin tayi, to sai dai wani matashi mai sharhi a harkokin siyasa ya bayyana dalilai 3 da yasa wasu daga cikin al'ummar Najeriya suke ganin gazawar gwamnatin shugaba Buhari.

1. A Lokacin yakin neman zabe shugaba Buhari ya bayyana kudurori da yawa ciki hada rage farashin man-fetur, sauke farashin kayayyaki abinci, samar da ayyukan yi, habaka harkar noma da kiwo da sauran kudurori; bayan Buhari ya dane kujera sai wasu daga cikin al'kawuran nashi suka gagara musamman fannin saukar da farashin kayayyaki masarufi da kuma na man-fetur.

2. Shugaban kasa Muhammad Buhari bai yi sa'an 'yan majalisun dattijai ba, hada na wakilai da sauran mukarraban gwamnatinsa ganin cewa manufar su daban yake da nashi.

Shin me nene Buhari ya yi a shekaru 2 da ta gabata ne?

Shugaba Muhammadu Buhari na rike da wata yarinya a ranar bikin yara

KU KARANTA: Gaskiya za ta fito: Dogarin Shugaba Abacha; Hamzah Al-Mustapha zai rubuta littafi

3. Tun da farko dai manyan kasar nan basa kaunar ganin Buhari a matsayin shugaban kasa, talakawa ne kadai ke da wanna burin kuma Allah ya karba addu'an su, kuma wadannan manyan zasu yi duk yadda zasu yi ganin sun durkusar da dukkan yunkurin gwamnatin Buhari na kawo duk wani ci gaba a kasar nan ta fannoni da dama kuma zasu iya kawo masa tikas wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari idan kuka lura da wadannan dalilan 3 lallai zaku gane al'ummar Najeriya baza su taba gane irin alherin da shugaba Buhari ya kawo kasar nan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Femi Fani Kayode ya bayyana hirar da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel