Toh fa: Shugaban majalisar dattawa ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya

Toh fa: Shugaban majalisar dattawa ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya

- Shugaban majalisar dokokin ya shawarci ‘yan siyasa cewa abin takaici ne ganin yadda suke gagwarmaya kan zaben 2019 tun yanzu

- Saraki yace ya kamata a cika wa ‘yan Najeriya alkawuran da aka yi masu kafin tunanin zaben 2019

- Shugaban majalisar ya kara da cewar suna yaki da cin hanci da rashawa a kasar dagan-dagan, ba gudu ba jabaya

Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Dakta Bukola Saraki, ya ce abin takaici ne ganin yadda ‘yan siyasa ke gwagwarmaya kan zaben 2019 tun yanzu. Shugaban ya kara da cewa ya kamata a mayar da hakali kan cika alkawuran da aka wa talakawa a lokacin yakin neman zaben da ta gabata a 2015.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Saraki ya bayyana cewa, shekarar 2019 yanzu dogon lokaci ne idan aka yi la’akari da kuma tunanin cewa shekaru biyu ne kawai suka yi cikin shekaru udu da zasu yi a mulki, ya ce abin kunya ne ganin yadda wasu ‘yan siyasa ke fafutukar yadda zaben 2019 zai kaya.

Da yake jawabi a lokacin wata hira da manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni, ya ce har yanzu gwamnati bata cika wasu daga cikin tsammanin 'yan Najeriya ba, ya kara da cewa ya kamata su mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma da kuma cika alkawurar da suka yi wa jama’a.

Toh fa: Shugaban majalisar dattawa ya caccaki ‘yan siyasan Najeriya

Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Dakta Bukola Saraki

KU KARANTA: Jama’an mazabar Kogi ta yamma sunyi bukaci INEC ta gudanar da zaben cire Dino Melaye

Shugaban majalisar ya ce: " Yanzu aka tattalin arzikin kasa ta fara farfadowa kan hanya, yanzu saura mu magance batun na tsaro. Muna yaki da cin hanci dagan-dagan; amma muna bukatar yin karin a wannan. In har muka ci gaba da hakan nan, toh, babu shaka nan da shekara, ina zaton cewa za mu iya yaba kanmu cewa mun yi kokari.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel