Gidauniyar Indimi Foundation ta raba kayan azumi ga ‘yan gudun hijira

Gidauniyar Indimi Foundation ta raba kayan azumi ga ‘yan gudun hijira

- Gidauniyar Indimi Foundation dake jihar Borno ta taimakawa ‘yan gudun hijira yayin da ta rarraba masu kayayyakin abincin

- Gidauniyar ta kashe kimani naira miliyan 70 wajen sayo kayayyakin abincin da ta raba

- Gidaunaiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin taimakawa mutanen da suka tsinci kansu cikin wannan masifa

Albarkacin watan Ramadan gidauniyar Indimi Foundation dake jihar Borno, ta taimakawa ‘yan gudun hijira da gajiyayyu da tallafin kudade da kayayyakin abincin na miliyoyin nairori.

Gidauniyar Indimi Foundation ta ce ta kashe naira miliyan 70 wajen sayo kayayyakin abincin da take rabawa, tana kuma raba kudade.

Gidaunaiyar ta ce sun dauki wannan mataki ne domin taimakawa mutanen da suka tsinci kansu cikin wannan masifa, wadanda wasu lokuta kan sha wahala wajen samun abin da zasu saka a bakinsu.

Gidauniyar Indimi Foundation ta raba kayan azumi ga ‘yan gudun hijira

Gidauniyar Indimi Foundation da ta raba kayan azumi ga ‘yan gudun hijira

Haka kuma gidauniyar ta mayar da hankali ga mata da kananan yara da rikin ‘yan kungiyar Boko Haram ya shafa.

KU KARANTA: Ruwa ya yi barna a sansanin ‘yan gudun hijira

Dayawa daga cikin ‘yan gudun hijirar da suka sami wannan tallafi na abinci da kudi sun nuna godiyarsu da jin dadinsu ga wannan taimako da kungiyar Indimi Foundation ta yi musu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa daraktar gidauniyar Hajiya Amina Indimi, ta ce Allah ne ya basu ikon kai taimakon zuwa sansanin ‘yan gudun hijira a wannan wata mai falala. Haka kuma ta ce zasu ci gaba da fita asibitoci da sansanin ‘yan gudun hijira domin isarwa da mabukata taimako.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel