Ruwa ya yi barna a sansanin ‘yan gudun hijira

Ruwa ya yi barna a sansanin ‘yan gudun hijira

- Ruwan sama da guguwa da aka yi a karshen mako sun lalata matsugunnan 'yan gudun hijirar Boko Haram a jihar Borno

- Mutun daya ya rasa ransa sanadiyar ruwan saman a sansanin 'yan gudun hijira na Bakasi da ke Maiduguri

- Akalla mutane 4,300 ne matsalar barnar ruwan ta shafa musamman a sansanin na Jere, Kaga, Konduga da Maiduguri

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da guguwa da aka yi a karshen mako nan a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun yi munmunar barna a matsugunnan 'yan gudun hijira wadanda yakin Boko Haram ya raba da gidajensu a cikin jihar Borno, inda har mutun daya ya rasa ransa a sansanin 'yan gudun hijira na Bakasi a Maiduguri.

KU KARANTA: Za a kafa dokar zaman gidan yari na wata 6 ga masu tsallake layi

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar wato OIM wacce ta sanar da hakan a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni ta ce mutane akalla 4,300 ne matsalar ta shafa musamman a matsugunnin 'yan gudun hijira na Jere da Kaga da Konduga da Maiduguri.

Ruwa ya yi barna a sansanin ‘yan gudun hijira

Matsugunnan 'yan gudun hijirar a jihar Borno

Hukumar ta OIM ta ce babban aikin da ta sa gaba a halin yanzu shi ne na gyara wuraren kwanciyar 'yan gudun hijirar da gina magudanan ruwa da kuma samar da ingantattun gine-gine wadanda 'yan gudun hijirar za su dinga fakewa a duk lokacin da hadari ya taso.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel