Wasu na kokarin karbe mulki daga hannun Osinbajo-Inji Fadar Shugaban kasa

Wasu na kokarin karbe mulki daga hannun Osinbajo-Inji Fadar Shugaban kasa

– Wasu ‘Yan Arewa sun zargi Osinbajo da danne sauran Jama’a

– A cewar su Yarbawa kurum da Kiristoci Osinbajo yake ba mukamai

– Fadar Shugaban kasa tayi watsi da wannan magana

An zargi Osinbajo da dora mutanen sa kadai tun da ya karbi mulki

Cewar su Yarbawa ne da Fastoci kawai ke cin karen su ba babbaka

Sai dai Fadar shugaban kasar ta musanya wannan zargi

Wasu na kokarin karbe mulki daga hannun Osinbajo-Inji Fadar Shugaban kasa

Daga yafiyar Buhari: Osinbajo ‘Yan uwan sa kurum ya sani-‘Yan Arewa

Wasu ‘Yan Arewa sun bayyana cewa Kiristoci musamman ‘Yan Darikar RCCG kawai mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yake nadawa a Gwamnati. A cewar su dai Yarbawa ne su ka cika mukaman da ake nadawa.

KU KARANTA: Buhari na samun sauki Inji Uwargidar sa

Shugaban kasa

‘Yan Arewa sun koka da Osinbajo

An zargi Osinbajo da nada Ministan kasuwanci Dr. Enelemah Okey ganin cewa shi ya gaje kujerar sa a cocin da yake jagoranci. Haka kuma dai an bayyana cewa kusan duk Ma’aikatan da ke Ofishin sa daga cocin RCCG su ke kuma akasarin su Yarbawa ne.

Fadar shugaban kasar dai ta musanya wannan zargi bayan da farko ta ki cewa komai. Fadar tace wasu ne kurum ke kokarin karbe mulkin kasar daga hannu Mataimakin Shugaban kasar bayan da Shugaba Buhari yayi tafiya domin ganin Likita.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kokarin Gwamnatin Buhari daga kafuwa zuwa Yau

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel