Ba zamu lamunci yunkurin kara farashin mai ba - NUPENG

Ba zamu lamunci yunkurin kara farashin mai ba - NUPENG

- Kungiyar NUPENG ta yi watsi tare da gargadi dangane da yunkurin kara

- Shugaban kungiyar ya ce bai kamata a gabatar da kudirin ba saboda halin kuncin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki

Kungiyar ma’aiktan mai da hako iskar gas ta Najeriya NUPENG, ta yi watsi tare da yin gargadi dangane da yunkurin kara farashin man fetur, karkashin wani kudiri da aka gabatarwa majalisar dattawan kasar.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran najeriya NAN, a Legas, Alhaji Tokunbo Korodo, shugaban kungiyar ta NUPENG reshen kudu maso yammacin kasar, ya ce bai kamata a gabatar da kudirin ba, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin kuncin rayuwa, saboda haka kungiyar hadi da dukkanin reshunan na kwadago, ba zasu taba amincewa da wannan yunkuri ba.

KU KARANTA KUMA: 'Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai' - Shugabannin Arewa

Ba zamu lamunci yunkurin kara farashin mai ba - NUPENG

Ba zamu lamunci yunkurin kara farashin mai ba - NUPENG

Karkashin kudirin, wanda Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ya gabatarwa zauren majalisar dattijan a ranar Juma’ar da ta gabata, za’a rika biyan harajin naira biyar, kan kowace lita, za’a kuma yi amfani da harajin ne, wajen gina manyan hanyoyi a sassan kasar.

Har ila yau kudirin ya bukaci rage wani adadi na kudaden da fasinjoji ke biya zuwa sassan kasar, a kuma dawo da manyan shin gayen da a baya aka kafa a manyan titunan gwamnatin tarayya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo kan yadda kayan marmari sukayi tashin gwauron zabi a kasuwanni saboda Ramadan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel