Mijina na samun sauki sosai sannan kuma zai dawo kasar nan ba da jimawa ba – Aisha Buhari

Mijina na samun sauki sosai sannan kuma zai dawo kasar nan ba da jimawa ba – Aisha Buhari

- Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewa mijinta na samun sauki sosai

- Ta ce zai dawo kasar nan ba da jimawa ba

- Ta yi godiya ga ‘yan Najeriya kan irin addu’o’I da suke yi ma mijinta

A ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta kaddamar da cewa mijinta, shugaban kasa na samun sauki sosai.

Ta ba al’umma tabbacin cewa yana samun sauki sannan kuma zai dawo kasar nan ba da dadewa ba.

Aisha Buhari ta kasance babbar bakuwa a darasin Ramadan na 23 da kungiyar Ansar-ud-deen (ADS) ta gabatar a Abuja inda babban mataimakiyarta Dr Hajo Sani, ta wakilce ta.

NAIJ.com ta tuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma birnin Landan ne a watan Mayu domin ci gaba da jinya watanni kadan bayan ya dawo daga dogon hutu da yayi a birnin Landan.

KU KARANTA KUMA: 'Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai' - Shugabannin Arewa

A cikin jawabin da Dr Sani ya saki a madadin Uwargidan shugaba Buhari, wacce ta tafi birnin Landan kimanin kwanaki 5 da suka wuce ta ce:

“Mijina na samun sauki sosai. Sannan kuma kwanan nan zai dawo kasar domin fara ayyukan sa.

“Ina godiya ga ‘yan Najeriya kan irin addu’o’in ga mijina. Don Allah kada ku gaza gurin addu’o’inku,” cewar ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel