'Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai' - Shugabannin Arewa

'Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai' - Shugabannin Arewa

- Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo na fuskantar suka kan wasu nade-nade da ya yi

- An zargi mukaddashin shugaban kasa kan nada Dr Okey Enelamah a matsayin ministan harkokin kasuwanci da zuba jari

- Har ila yau an zarge sa a kan matsayi da y aba Alex Okoh

Wasu shugabannin Arewa sun soki mukaddashin shugaban kasa kan nade-nade da yayi wanda suke ganin akwai san kai da nuna bambanci.

Tun a makonni da suka gabata ne shugabannin Arewa suka fara cece-kuce game da nade-naden mukaddashin shugaban kasa.

Wata kasida da wani dan arewacin kasar ya rubuta kan mukaddashin shugaban kasar na tayar da kura a fagen siyasar kasar.

'Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai' - Shugabannin Arewa

Shugabannin Arewa sun ce Osinbajo na nuna bambanci wajen nadin mukamai

A cikin kasidar marubucin wanda ya kira kansa Dr. Ismaila Faruk daga jihar Zamfara, ya zargi Farfesa Yemi Osinbajo da nuna banbamci wajen nade naden mukamai.

Marubucin ya yi zargin cewa Osinbajo na amfani da damar da ya samu wajen nada 'yan kabilarsa ta yarbawa da kuma mabiya majami'ar sa kan manyan mukamai.

KU KARANTA KUMA: Wasu matasa sun kashe wata mata mai ciki saboda zargin maita a jihar Adamawa

Haka kuma murubucin ya ce hakan ya saba wa tanade tanaden kudin tsarin mulki.

Wasu masu sharhi a Najeriyar irin su Malam Bashir Baba, na ganin ba sabon abu ba ne ga masu rike da mukamai daga wasu shiyyoyi su rika aiwatar da muradun a'ummomin su sabanin yadda lamarin ya ke ga wasu masu rike da mukamai da suka fito daga arewacin kasar.

Sai dai ofishin mukaddashin shugaban ya yi fatali da wannan zargin.

Mataimakiya ta musamman kan harkokin shari'a ga muƙaddashin shugaban Nigeria Dr Bilkisu Sa'idu Babban ta bayyana cewa babu gaskiya a wannan zargi.

Ta ce: ''Akasarin manyan ma'aikatan dake tare da mukaddashin shugaban kasar 'yan arewa ne'', inji ta.

Ta bada misali da wasu mukamai a ofishin Osinbajo, inda ta ce masu wannan zargi kokari kawai suke yi su bata sunan mukaddashin shugaban kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon Osinbajo da ya ke ba da bayani a kan yakin Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel