Wasu matasa sun kashe wata mata mai ciki saboda zargin maita a jihar Adamawa

Wasu matasa sun kashe wata mata mai ciki saboda zargin maita a jihar Adamawa

- An yi ma wata mai ciki duka har lahira a kauyen Falu, jihar Adamawa

- An kama mutane biyar da ake zargin suna da alaka da mutuwar ta

- Matasan sun kai hari ga mai ciki da aka ambata da suna Ayina Afraimu kan zargin cewa tana da maita

Wata mata mai ciki mazauniyar garin Falu dake karamar hukumar Guyuk ta rasa ranta sanadiyar duka da tasha wajen mutanen garin kan zargin maita da akayi mata.

Kwamishinan rundunar ‘Yan sandan Jihar Moses Jitoboh ne ya sanarwa manema labarai haka a garin Adamawa.

Moses ya ce wasu matasa ne suka far ma wannan mata inda sukayi ta dukan ta da sanduna sannan suka daddaure ta da igiya.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kaduna, tare da iyalansa

“Matasan sun zarge ta da maita inda suka danganta rashin lafiya da mutuwar wasu mutane a kyauyen da ita.

“Wadanda suka aikata hakan sun hada da Abraham Adamu, 18, Malachi Yilafane, 35, Thomas Aji, 54, Zakariya Chorum, 56 da wata Newana Ilihal ‘yar shekara 20.”

An kuma yi nasarar cafke matasan guda biyar da ake zargin suna da nasaba da mutuwar mai cikin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel