Yadda wani mai yankan kumba yayi lalata da dan almajiri a jihar Bauchi

Yadda wani mai yankan kumba yayi lalata da dan almajiri a jihar Bauchi

Jami’ an yan sanda jihar Bauchi suna neman wani mai yankan kumba ruwa a jallo bayan yayi luwadi da wani dan almajiri a karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

Jami’an yan sandan sunce mutumin ya aikata wannan aika-aika ne a shekarar 2016, inda y aba dan almajirin mai suna Umar Ali,N40 kuma yace masa kada ya fadawa kowa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Haruna Mohammed, a wata jawabi da ya saki ranan asabar yace ba’a kawo karan zancen ofishin yan sandan ba sai ranan 17 ga watan Mayu, 2017 misalin karfe 4 na yamma.

Game da cewar Mohammed, bayan abinda ya faru cikin yaron ya fara kumbura. An dau dukkan wani mataki na asibiti amma a banza.

Yadda wani mai yankan kumba yayi lalata da dan almajiri a jihar Bauchi

Yadda wani mai yankan kumba yayi lalata da dan almajiri a jihar Bauchi

Yace: “ Bincike ya nuna cewa wani mai yankan kumba ne ya aikata wannan laifi a shekaran 2016.

“Tun lokacin ba’a kawo karan laifin ofishin yan sand aba. Kawai sai ya fara rashin lafiya cikinsa ya fara kumbura.

KU KARANTA: Janar Bamaiyi ya tona asirin Yemi Osinbajo

“An kaishi babban asibitin Darazo domin jiny amma ba sauki sannan aka mayar da shi asibitin jami’ ar ATBU domin jinya.”

Kakakin hukumar ya kara da cewa kwamishanan yan sandan jihar ya umurci mataimakin kwamishanan su tabbatar da cewa sun nemo mutumin.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel